1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages


 

Labarai | 30.07.2010

Wasu 'yan Kenya sun gurfana a gaban kotun Yuganda

 

An gurfanar da wasu 'yan Kenya a gaban kotu, bisa harin birnin Kampala.

 

An gurfanar da wasu 'yan asalin ƙasar Kenya a gaban kotun majistare a Yuganda, bisa zargin aikata laifukan kisan kai har 76 da ke da nasaba da harin ƙunar baƙin wake da aka kai birnin Kampala a ranar 11 ga watan Juli. Mutanen da aka gurfanar ɗin dai sune, Hussaini Hassan Agad da Mohammed Adan Abdow da kuma Idris Magondu. Ana dai cajin su ne da hannu a wancan harin bama-bamai da ya halaka  mutane da dama a wani wajen kallon wasan ƙwallon ƙafa na duniya da aka gudanar a Afirka ta Kudu. Tuni dai alƙalin kotun  ya ba da umarnin a ci gaba da tsare su, kafin a miƙa shari'ar a gaban wata babbar kotu. Yanzu dai a ranar 27 ga watan  Augusta ne dai mutanen uku za su sake gurfana a gaban kotun. Yanzu haka dai akwai 'yan ƙasar waje da dama da ake tsare da su dangane da wannan hari da ƙungiyar al-Shabab ta Somaliya ta ɗauki alhakin kai shi.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas

 

Halimatu Abbas

 

Send us an e-mail »Send »Print »

More on the topic

 
Share this article


 
Bikin kiɗa na Beethoven a Bonn

Bundesliga 2010/2011
Bajamushe a Wurin Aikinsa

Shiri kan rayuwa a Jamus - Na harshen Hausa a cikin shirye-shiryenmu kowace Talata da Alhamis.

DW-TV EUROPE live

Politik direkt

We're sorry, due to legal issues this content can not be transmitted as live stream.

If you are inside the United States, it is still possible for you to enjoy DW-TV. For more information, please click here.